An gabatar da Seyyed Mohammad Hosseinipour, wanda ya zo na daya a fagen nazarin karatun kur'ani mai tsarki na kasa karo na 46. A ranar karshe ta bikin ya karanta aya ta 72 zuwa ta 78 a cikin suratul Nisa’i.
A ranar Talata 5 ga watan Disamba ne aka gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta kasa karo na 46 na cibiyar Awqaf a bangaren mata na rukuni na 20 da ke Bojnoord da ke lardin Khorasan ta Arewa.