IQNA

Yahudawa sun kai hari kan masu ibadar masallacin Al-Aqsa da hayaki mai sa hawaye a safiyar ranar Qudus

16:08 - April 05, 2024
Lambar Labari: 3490931
IQNA - Da sanyin safiyar yau ne sojojin yahudawan sahyuniya suka kaiwa masallatan da suka halarci sallar asubahin Juma'ar karshe na watan Ramadan a masallacin Al-Aqsa da hayaki mai sa hawaye.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Larabci Boost cewa, shaidun gani da ido sun bayyana cewa, sojojin mamaya sun harba barkonon tsohuwa kan masu ibada a gaban masallacin Qubali ba tare da wani gargadi ba.

A baya dai gwamnatin yahudawan sahyuniya ta sanar da aikewa da dakarun soji 3,600 domin kula da halin da ake ciki a masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus a ranar Juma'ar karshe ta watan Ramadan. Ana sa ran sama da mutane 60,000 ne za su halarci sallar Juma'a a wannan masallaci mai albarka.

Majiyar cikin gida ta bayar da rahoton cewa, dubban Falasdinawa masu ibada sun yi ta rera taken nuna goyon baya ga zirin Gaza da kuma masallacin Al-Aqsa bayan harin da sojojin yahudawan sahyoniya suka kai.

A cewar shaidun gani da ido, an harba hayaki mai sa hawaye da wani jirgin sama mara matuki na sahyoniyawan da ke shawagi a sararin samaniyar masallacin. Sun lura cewa daga baya hankali ya koma harabar masallacin Al-Aqsa.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin yahudawan sahyoniya ba ta ce uffan kan dalilan da suka sanya suka jefar da masu ibadar hayaki mai sa hawaye ba.

Fim na asali

Ma'aikatar Dokokin muslunci ta Kudus a cikin wata sanarwa da ta fitar ta bayyana cewa: Kimanin mutane dubu 65 ne suka gudanar da sallar asubahin Juma'a a masallacin Al-Aqsa kuma dubun dubatar masu ibada na shirin gabatar da sallar Juma'ar karshe ta watan Ramadan a masallacin Al-Aqsa. .

Juma'ar karshe ta watan Ramadan na wannan shekara ta zo daidai da daren 26-27 ga watan Ramadan, wannan dare shi ne dare daya tilo a cikin shekarar da ake bude kofofin masallacin Aqsa ga masu ibada duk dare da rana.

 

 
 

 

 

captcha