IQNA

Allah ya yi wa wani shahararren makarancin kur'ani dan kasar Masar a Amurka

16:40 - April 28, 2023
Lambar Labari: 3489052
Tehran (IQNA) Shahararren makaranci dan kasar Masar Sheikh Abdullah Kamel da ya je kasar Amurka domin gudanar da ibadar azumin watan Ramadan, ya rasu a yau sakamakon bugun zuciya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aljazeera cewa, masallacin Al-Tauhid da ke birnin Jersey na kasar Amurka ya sanar da rasuwar wannan makaranci dan kasar Masar tare da buga wani rubutu a shafinsa na Facebook inda ya rubuta cewa: Mu daga Allah muke kuma zuwa gare shi za mu koma. Cikin bakin ciki muke sanar da rasuwar Abdullahi Kamil, wanda ya jagoranci Sallar Tarawihi a shekarar da ta gabata da kuma na bana. Ya koma ga Ubangijinsa kuma rashinsa ya yi tasiri matuka ga al’ummarmu.

Wannan cibiya ta kara da cewa: Ya kasance mashahurin mai karatun kur'ani mai tsarki a duniya, kuma karatunsa abin ta'aziyya ne ga dukkan mu, kuma muryarsa ta cika zukatanmu da kaunar Ubangiji, kuma za mu rika tunawa da kyawawan karatunsa. Muna mika ta'aziyyarmu ga iyalansa bisa wannan rashi.

Sheikh Kamel ya kasance sanannen mai magana da karatun kur'ani kuma makaho ne. An haife shi ne a lardin Fayum na kasar Masar a shekarar 1985, kuma ya kammala haddar dukkan kur'ani a makafi tun yana karami, sannan ya kammala karatunsa na digiri na biyu a fannin kimiyya a jami'ar Fayum a shekarar 2005.

Ya halarci gasa da dama a karatun Al-Qur'ani kuma baya ga tashar YouTube, yana da shirye-shiryen bidiyo da yawa a cikin yanar gizo.

Kamel ya halarci shirye-shiryen addini da dama ta tashoshin tauraron dan adam, ya kuma zagaya kasashe da dama da suka hada da Kuwait, Saudiyya da Amurka domin karanta kur'ani da gabatar da sallah. An watsa karatunsa na kur'ani a gidan talabijin na kasashen Larabawa.

 

 

4136911

 

captcha