IQNA

Miliyoyin Masu Ziyara a Karbala a jajibirin Arbaeen

16:11 - September 16, 2022
Lambar Labari: 3487862
Tehran (IQNA) Birnin Karbala yana cike da maziyarta da suka zo wannan birni mai alfarma daga larduna daban-daban na kasar Iraki da wasu kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Al-Furat na kasar Iraki ya fitar da hotunan yadda miliyoyin masu ziyara ke halartar haramin Imam Husaini (a.s.) da kuma Sayyid Abbas (a.s) da kuma tsakanin hubbarori da ke Karbala domin ziyarar arbaeen.

Wadannan hotuna suna da alaka da yammacin ranar Alhamis 18 ga watan Safar, kuma sun nuna halartar miliyoyin maziyarta Imam Hussaini a Karbala a jajibirin Arbaeen.

Dangane da haka, Manjo Janar "Saad Ma'an" shugaban cibiyar tsaron kasar Iraki ya sanar da cewa adadin maziyarta da suka halarci taron Arbaeen a wannan shekara shi ne mafi girma tun daga shekara ta 2003.

Ya kara da cewa: Rundunar hadin guiwa ta tabbatar da cewa ba a samu labarin wata matsala ta ta’addanci ko tsaro ba a lokacin Arbaeen , ko kuma a kan hanyoyi da ya shafi ababen hawa.

 

 

4085906

 

 

captcha