Shafin Aljadeed ya bayar da rahoton cewa, wani katafaren shagon sayar da kayan masarufi a birnin Beirut na Lebanon ya ki amincewa ya dauki wata ma'aikaciya saboda lullubi da take sakawa a kanta.
Sumayya Hijazi wata marubuciya ce a shafukan sada zumunta, ta bayyana cewa shagon ya kori matar da ya dauka aiki bayan da ta zo da lullubi, sanann ya maye gurbinta da wata sabuwar ma'aikaciya wadda ba ta saka lullubi.
Duk da cewa shagon ya bai bayyana wata mummunar dabi'a ko wani aiki na sabawa kaidarsa da mai saka lullubin ta yi ba, amma ya kore ta ba tare da bayyana dalili ba.
Daga bisani shagon ya sanar da dewa, ya dauki matakin ne saboda tana saka lullubi, wanda ya sabawa abin da ake bukata a wurin.
Mutane da dama a kasar vta Lebanon suna ci gaba da mayar da martani dangane da wannan lamari, inda ake yin kira da a kauracewa yin sayayya a wurin, saboda nuna kyamar tufafin mulunci da shagon ya nuna a zahiri.
https://iqna.ir/fa/news/4033705