Bangaren yada labarai na hubbaren Karbala ya sanar da cewa, bayan sanar da janye dokar hana taruka saboda kaucewa yaduwar cutar corona an gudanar da sallar jam'i ta farko farfajiyar hubbaren Imam Hussain (AS) da ke birnin na Karbala.
Mutane da dama ne suka halarci wannan sallar jam'i inda aka sallolin Azuhur da La'asar, duk kuwa da cewa har yanzu akwai ka'idoji da aka gindaya na kiwon lafiya, wanda ya zama wajibia kiyaye su.
Sheikh Salah Karbala'i babban malami mai kula da harkokin hubbaren shi ne dai ya jagoranci limancin sallolin.