IQNA

Ana Gudanar Da Zaben 'Yan Majalisar Dokoki A Yau A kasar Iraki

17:30 - October 10, 2021
Lambar Labari: 3486409
 Tehran (IQNA) A rana yau ce al'ummar kasar Iraki suke kada kuri'a a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Mawazin News ya habarta cewa, yau ne ake gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki a kasar Iraki, inda aka bude rumfunan zabe tun da safiyar yau Lahadi.

Rahotanni daga kasar ta Iraki sun ce, shugaban kasar Barham Saleh, da firayi minista Mustafa Alkazimi, da shugaban majalisar dokoki Muhammad Alhalbusi, gami da mayna ‘yan siyasa da masu karfin fada ajia kasar duk sun kada kuri’unsu.

Mai magana da yawun hukumar zaben kasar Iraki Jumana Alghawi ta bayyana cewa, adadin rumfunan zabe a fadin kasar sun haura dubu 55, yayin da kuma masu sanya ido na kasa da kasa a wannan zabe adadinsu ya kai 1249, sai kuma ‘yan jarida 510 ne suka shigo kasar daga kasashen duniya domin bayar da rahotanni kan zabe.

Adadin ‘yan takarar kuma ya kai 3227, da suka hada da mata 951, sai kuma Hadaka 21 gami da jam’iyu109.

Akalla mutane milyan 25 ne aka tantance wadanda suke kada kuri’unsu a zaben ‘yan majalisar na a kasar Iraki.

A cikin shekara ta 2022 ne ya kamata a gudanar da wannan zabe, samakon matsalolin da kasar ke fama da su, da jama’a suka nuna rashin amincewa da yadda lamurra ke tafiya, hakan yasa ala tilas a gudanar da zabe kafin wa’adin aka ayyana.

 

 

4003543

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: shekara rashin amincewa
captcha