IQNA

Nasrullah: Wargaza Kasar Lebanon Na Daga Cikin Dalilan Kirkiro 'Yan Ta'addan Daesh

20:13 - August 28, 2021
Lambar Labari: 3486248
Teharan (IQNA) Babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa wargaza kasar Lebanon da syria na daga cikin dalilan kirkiro Daesh.

Shafin yada labarai na al'ahad ya bayar da rahoton cewa, babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, an yi niyyar haddasa yaki a Lebanon da Syria ne a lokaci guda, amma sadaukarwar sojojin kasar da kuma Hizbullah da sauran bangarorin ‘yan gwagwarmaya ne ya hana aukuwar hakan a Lebanon.

A lokacin da yake gabatar da jawabi a daren jiya, dangane da cikar shekaru 4 da kammala tsarkake yankin Jurud da ke gabashin kasar Lebanon daga ‘yan ta’addan Takfir, Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, an shirya ragargaza kasashen Syria da Lebanon ne a lokaci guda tun daga lokacin da aka haddasa yaki a kasar Syria.

Sayyid Nasrullah ya ce, dukkanin abin da ya faru a kasar Syria a cikin shekaru 10 da suka gabata, abu ne tsararre, wanda wasu kasashe suka zauna suka shirya shi, da nufin ganin sun rusa kasar baki daya, gami da kasar Lebanon wadda take makwabtaka da kasar ta Syria.

Ya ci gaba da cewa, Amurka da wasu daga cikin kasashen turai gami da wasu ‘yan korensu daga cikin gwamnatocin larabawa ne suka shirya dukkanin abin da ya farua kasar Syria, inda suka kwaso dubban daruruwan ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi daga kashen duniya zuwa Syria domin aiwatar da wannan manufa.

Ya ce shigowar ‘yan ta’addan Daesh a cikin yankin Jurud na gabashin kasar Lebanon daga kasar Syria na daga cikin shirin da aka yi, daga nan kuma za su ci gaba da ayyukan ta’addanci kamar yadda suka yi a Syria domin rusa kasar Lebanon.

Sayyid Nasrulla ya ce wannan ya sanya kungiyar Hizbullah ta yi amfani da karfinta wajen taimaka wa sojojin kasar Lebanon wajen murkushe wadannan ‘yan ta’adda, tare da tsarkake dukkanin yankunan da suka kame a gabashin kasar Lebanon, ta yadda gwamnatin kasar ta samu damar sake shimfida ikonta a wadannan yankuna.

 

3993355

 

captcha