IQNA

Dakarun Hashd Alshaabi Na Iraki Sun Samu Nasarar Fatattakar 'Yan Ta'addan Daesh Daga Yankin Tarimiyyah

21:35 - August 24, 2021
Lambar Labari: 3486236
Tehran (IQNA) dakarun sa kai na al'ummar kasar Iraki sun samu nasarar fatattakar mayan 'yan ta'addan daesh daga yankin Tarimiyyah.

Shafin yada labarai na Mawazin News ya bayar da rahoton cewa, a farmakin da dakarun sa kai na al'ummar kasar Iraki tare da hadin gwiwa da jami'an tsaron kasar suka kaddamar, sun samu nasarar fatattakar mayan 'yan ta'addan daesh daga yankin Tarimiyyah da ke arewacin birnin Bagadaza fadar mulkin kasar.

Tun a ranar Talatar makon da ya gabata ce aka fara kaddamar da wannan farmaki, bayan samun bayanai na sirri dangane da ayyukan da 'yan ta'adda suke aiwatarwa a yankin.

Tare da taimakon al'umma da suke bayar da hadin kai wajen fallasa 'yan ta'addan, an samu aggarumar nasara wajen tarwatsa su.

Ni'amah alkufi mataimakin babban kwamandan dakarun Hashd Alshaabi a  bangaren gudanarwa ya bayyana cewa, a cikin lokutan baya-bayan nan 'yan ta'addan suna neman sake dawo da ayyukansu a wasu yankuna na Iraki, amma da daimakon Allah ba za su cimma nasara ba.

A farmakin Tarimiyyah ana kashe adadi mai yawa na 'yan ta'adda tare da kame wasu da jikkata wasu, wadanda yanzu haka suna hannun hukuma, za su gurfana a gaban kuliya.

3992723

 

 

captcha