Tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, kungiyar Hizbullah ta fitar da bayani a yau Juma'a da cewa, kungiyar ce ke da alhakin harba makaman roka a yau a kan sansanonin sojin Isra'ila, sakamakon harin da Isra'ila ta kai jiya a kudancin Lebanon.
Bayanin ya ce, da misalin karfe 11:15 na safiyar yau Juma'a, dakarun kungiyar ta Hizbullah sun harba makaman roka a kan sansanonin sojin Isra'ila, a matsayin martani kan shishigin da Isra'ila ta yi kan kasar Lebanon, kuma idan Isra'ila ta ci gaba da abin zai biyo baya a kanta zai fi haka.
Kafofin yada labaran Isra'ila sun ce an harba makaman ne daga kasar Lebanon zuwa yankunan wadanda sojojin Isra'ila suka kafa sansanoninsua yankin Jalil da kuma Tuddan Golan.
Malaman kudancin Lebanon sun fitar da sanarwa da ke nuna cikakken goyon bayansu ga matakin na kungiyar Hizbullah, tare da jaddada cewa wannan shi ne kawai mafita, a duk da Isra'ila ta yi shishigi kan Lebanon to ita ma ta dandana kudarta.