IQNA

Wani Babban Jirgin Ruwan Isra'ila Na Ci Da Wuta Bayan An Kai Masa Hari A Cikin Teku

16:36 - July 04, 2021
Lambar Labari: 3486074
Gwamnatin yahudawan Isra’ila ta sanar da cewa an kai wa wani katafaren jirginta na ruwa hari a cikin tekun India.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, majiyoyin gwamnatin yahudawan Isra’ia sun sanar da cewa, an kai wa katafaren jirgin ruwan hari ne a lokacin day a yake kan hanyarsa ta zuwa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa daga gabar ruwan Jiddah a kasar Saudiyya.

Jirgin yahudawan dai yana dakon danyen man fetur ne, wanda kuma mallaki na kamfanin Isra’ila, inda kuma har yanzu babu wata kungiya ko wani bangare da ya sanar da alhakin kai harin.

Sai tuni jami’an gwamnatin yahudawan Isra’ila suka sanar da cewa, suna gudanar da bincike domin tabbatar da cewa ko Iran tana da hannu a cikin lamarin.

captcha