IQNA

An Sanar Da Matakai Na Kaucewa Yaduwar Corona A Cikin Watan Ramadan A Masar

19:05 - April 02, 2021
Lambar Labari: 3485776
Tehran (IQNA) mahukuntan kasar Masar sun sanar da matakai da za a dauka a cikin watan azumi domin kaucewa yaduwar cutar corona.

Shafin yada labarai na jaridar Alahram ta kasar Masar ya bayar da rahoton cewa, mahukuntan kasar sun sanar da matakai da za a dauka a cikin watan azumi domin kaucewa yaduwar cutar corona a tsakanin jama’a.

Bayanin ya za a iya gudanar da sallolin nay au da kullum a cikin masallatai, da kuma sallar asham, amma kada lokacin gudanar da ita ya wuce mintuna talatin, sannan kuma babu batun gudanar da sallar tahajjud a masallatai.

Baya ga haka kuma, an hana gudanar da buda baki da cibiyoyi suke dauka wanda daruruwa ko dubban mutane suke halarta, kamar yadda kuma shaguna za asu iya kasancewa a bude har zuwa 11 na dare, wuraren cin abinci kuma za su iya kaiwa har karfe daya na dare.

Shekarar 2020 da ta gabata, gwamnatin kasar Masar ta hana gudanar da sallar tarawihi ko asham a dukkanin masallatan da ke fadin kasar, in ba da wasu ‘yan kalilan daga cikinsu.

 

3961858

 

 

 

 

 

captcha