IQNA

Musulmin Kasar Myanmar Suna Bayar Da Gudunmawa Wajen Yaki Da Corona

23:02 - December 15, 2020
Lambar Labari: 3485462
Tehran (IQNA) musulmin kasar Myanmar suna bayar da gudunmawa wajen yaki da cutar corona a kasar.

Musulmin kasar Myanmar wadada su ne marassa rinjayea  kasar wadda akasarin mutanenta mabiya addinin Buda ne, suna bayar ad gudunmawa wajen yaki da cutar corona.

Wasu gungun musulmin kasar ta Myanmar ne suke bayar da dukkanin lokacinsu wajen hada karfi da sauran bangarori na kiwon lafiya a kasar, domin taimaka ma jama'a wajen yaki da cutar corona, da hakan ya hada da daukar marassa lafiya da kai su asibitoci da kuma kula da su.

Idan ba manta ba dai musulmin kasar Myanmar suna fuskantar wariya da ake nuan musu saboda addininsu, inda aka kashe dubbai daga cikinsu da kuma mayar da wasu dubban daruruwa 'yan gudun hijira a kasashe makwabta.

3940907

 

captcha