IQNA

Saudiyya Ta Tabbatar Da Harin Martani Da Dakarun Yemen Suka Kai Kan Aramco

23:08 - November 24, 2020
Lambar Labari: 3485395
Tehran (IQNA) Saudiyya ta tabbatar da aukwar hare-haren martani da sojoji gami dakarun sa kai na al’ummomin Yemen suka kai kan kamfanin Aramo.

A cikin wani bayani da ya fitar a yau, maimagana da yawun kawancen Saudiyya da ke kaddamar da yaki a kan al’ummar kasar Yemen Turki Maliki, ya bayyana cewa da jijjifin safiyar a jiya Litinitin, mayakan Alhuthi sun harba makamai a kan cibiyar mai ta kamfanin ARAMCO a Jidda.

Ya ce harin ya jawo gobara  a wasu bangarorin cibiyar, amma jami’an kwana-kwana sun samu nasarar kashe wutar da ta tashi daga bisani, kuma babu wani wanda ya rasa ransa ko jikkata sakamakon harin.

A safiyar jiya ne kakakin rundunar sojin Yemen karkashin gwamnatin san’a Brig Gen. Yahya Sari ya sanar da cewa, sun kaddamar da wasu hare-haren ramuwar gayya a kan kamfanin main a ARAMCO a garin Jiddah, a matsayin martani kan munanna hare-haren da Saudiyya take kaddamarwa   akan al’ummar kasar Yemen.

Bisa ga rahotannin da majalisar dinkin duniya da kungiyoyin agaji na duniya masu zaman kansu suka harhada, daga shekara ta 2015 da Saudiyya ta fara kaddamar da hari kan al’ummar kasar Yemen ya zuwa yanzu, ta kashe dubban fararen hula, galibinsu mata da kananan yara, tare da rusa daruruwan masallatai, makarantu, kasuwanni, asibitoci da dubban gidajen jama’a.

 

3937021

 

 

captcha