IQNA

Qalibaf: Keta Alfarmar Ma'aiki (SAW) Keta Alfarmar Annabawan Allah Ce Da Dukkanin Bil Adama

20:33 - October 30, 2020
Lambar Labari: 3485320
Tehran (IQNA) kakakin majalisar dokokin Iran ya bayyana cin zarafin Annabi a matsayin cin zarafin dukkanin Annabawan Allah baki daya.

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewar cin zarafin Annabi yana a matsayin cin zarafin dukkanin Annabawa da kuma saukakkun Littafa na Ubangiji ne, yana mai cewa kulla alaka ta diplomasiyya da haramtacciyar kasar Isra’ila da wasu ‘yan tsirarrun kasashen musulmi suka yi babu wani tasiri da zai yi ga gwagwarmayar al’ummar Falastinu kamar yadda kuma hakan ba abu ne tabbatacce ba.

Qalibaf ya bayyana hakan a jawabin da yayi yayin bude taron makon hadin kan al’ummar musulmi karo na 34 da aka gudanar a nan birnin Tehran inda ya ce: Cin zarafin Annabi yana a matsayin cin zarafin dukkanin Annabawa da kuma saukakkun Littafa na Ubangiji ne. Duk wani mutum ko kuma wata cibiyar da ta aikata hakan kuwa toh ba ta san inda aka sa gaba ba.

A wani bangare na jawabin nasa, shugaban majalisar shawarar Musulunci ta Iran ya tabo batun Falastinu a matsayin wani lamari wanda musulmi suka yi ittifaki kansa a matsayin wani hakki na al’ummar Falastinu, don haka sai ya ce; shugabannin kasashen da suka kulla alaka da Isra'ila su san cewa wannan kawance na su ba zai jima ba, to amma abin kunya da bakin cikin hakan zai ci gaba da binsu tsawon tarihi.

A yau ne dai aka fara gudanar da bukukuwan makon hadin kan al’ummar musulmi don tunawa da ranar da aka haifi Fiyayyen halitta, Manzon Allah kamar yadda marigayi Imam Khomaini, wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bukata kuma ya sanya wa wadannan ranakun makon hadin kai.

3931970

 

 

captcha