Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da kungiyar kasashen musulmi ta OIC ta fitar, ta bayyana kona kur’ani mai tsarki da aka yi a kasar Sweden na a matsayin wani sabon yunkuri na nuna tsananin kyama da gaba ga addinin muslunci.
Bayanin ya ce irin wannan mataki ba a bu ne da zai haifar da zaman lafiya a duniya ba, a kan haka ya zama wajibi kan gwamnatocin da ake aikata haka a cikin kasashen su gaggauta daukar matakan hana sake faruwar irin haka, tare da kamo dukkanin wadanda suke da hannua cikin wannan aika-aika a gurfanar da su a gaban kuliya domin su fuskanci hukunci.
Ita ma a nata bangaren cibiyar Ahhar a kasar Masar ta fitar da nata bayanin, wanda yin tir da Allawadai da kakausar murya kan wanann mummunan aiki.
A daya bangaren kungiyoyin musulmi da ma fitattun mutane a duniya suna ci gaba da mayar da martani kan wannan aiki na tsokana da masu tsananin kiyayya da musulmi suka aikata a Sweden, da kuma tunzura sauran masu akida irin tasu a kasashen turai domin su aikata hakan, inda lamarin ke shan kakkausar suka da Allawadai, da kuma neman a dauki mataki a kan masu aikata hakan.