IQNA

Dakarun Hashd Sha’abi Sun Cafke Wasu Kwamandojin Daesh Biyu

23:35 - May 25, 2020
Lambar Labari: 3484836
Tehran (IQNA) dakarun sa kai na al’ummar Iraki masu yaki da ‘yan ta’adda sun samu nasarar cafke wasu giggan ‘yan ta’addan Daesh biyu.

Shafin yada labarai na al’maluma ya bayar da rahoton cewa, Abu Haidar Altaibawi, daya daga cikin manyan kwamndojin dakarun sa kai na al’ummar Iraki masu yaki da ‘yan ta’adda ya sanar da cewa, sun samu nasarar yi wa ‘yan ta’addan Daesh kwantan bauna a cikin gundmar Falluja, sun cafke wasu manyan kwamandojin ‘yan ta’addan biyu da ake nema.

Ya ce wadannan giggan ‘yan ta’adda sna da hannu wajen shirya hare-hare da dama da mayakan ‘yan ta’addan Daesh suka kaddamar a cikin Iraki, inda suka kashe fararen hula da dama.

Al-taibawi ya ce kame wadannan manyan ‘yan ta’addan wata babbar nasara ce a gare su, domin hakan zai taimaka wa jami’an tsaro wajen samun wasu muhimman bayanai da ake bukata a ayyukansu na yaki da ‘yan ta’adda a cikin kasar ta Iraki.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3901203

 

Abubuwan Da Ya Shafa: dakarun sa kai hashd sha’abi iraki
captcha