IQNA

Dakarun Hadin Gwiwa Na Iraki Sun Fara Kaddamar Da Farmaki Kan Iyakokinsu Da Syria

23:54 - April 27, 2020
Lambar Labari: 3484751
Tehran (IQNA) dakarun hadin gwiwa na kasar Iraki sun fara kaddamar da wani farmaki a kan mayakan ‘yan ta’adda na Daesh a kan iyakokin kasar da kuma Syria.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Ahmad Nasrullah kakain rundunar mayakn sa-kai na Hashd Sha’abi, tare da hadin gwiwa da rundunar sojin kasar  Iraki, sun fara gudanar da wani shiri na tsarkake kan iyakokin kasar da Iraki.

Rahoton ya ce wannan farmaki na zuwa ne bayan samun cikakken bayani kan yunkurin mayakan ‘yan ta’addan daesh na sake neman dawowa cikin kasar Iraki bayan fatattakarsu.

Kafin wannan lokacin wasu rahotanni sun tabbatar da cewa, an ga wasu daga cikin mayakan ‘yan ta’addan na Daesh a cikin lardin Anbar da ke iyaka da Syria dauke da makamai.

3894808

 

 

captcha