Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Anatoli cewa, gwamnatin Saudiyya ta kirayi zaman gaggawa na kungiyar kasashen musulmi dangane ad yunkurin Isra’ila na hade yankunan gabar yamma da kogin Jordan.
Wannan mataki na saudiyya na zuwa ne bayan barazanar da firayi ministan Isra’ila ya yi ne kan cewa idan ya lashe zabe mai zuwa wanda za a gudanar a ranar 17 ga wannan wata na Satumba, zai hade yankunan gabar yamma da kogin Jordan da sauran yankunan Isra’ila.
Wannan furuci dai yana ci gaba da fuskantar martani daga ko’ina cikin fadin duniya, da hakan ya hada har daga manyan kawayen Isra’ila daga cikin kasashen larabawa.
A cikin yankunan falastinawa na gabar yamma da kogin Jordan dai a halin yanzu akwai matsugunnan yahudawa guda 250, inda yahudawa dubu 400 suke zaune a cikinsu.