IQNA

An Nuna Kur’ani Bugun Kasar Iran A Baje Kolin Littafai Na Thailand

23:43 - April 05, 2018
Lambar Labari: 3482541
Bangaren kasa da kasa, an nuna kwafin kur’ani bugun kasar Iran da ma wasu littafai na addini da aka bugar  a kasa a babban baje kolin kasa da kasa a Thailand.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wurin babban baje kolin kasa da kasa a da ke gudana yanz haka a kasar Thailand an nuna kwafin kur’ani bugun kasar Iran da ma wasu littafai na addini da aka buga  a kasar.

Wannan kur’ani yana dauk da tarjama a cikin harshen farisanci wanda Mahdi Ilahi Qhomshe ya tarjama, kuma ake amfani da shi a bangarori daban-daban na ilimi.

An yi amfani da fasahar rubutu wajen rubuta kur’anin kuma tarjamarsa da ke gefea  cikin harshen farisanci, wanda masu amfani da harshen suke amfani da wannan kur’ani domin gane ma’anonin ayoyi da tarjamarsu a makarntu da ma jami’oi.

Baya ga kwafin kur’anin da aka rubuta a Iran, an kuma nuna wasu daga cikin littafan da aka rubuta kuma aka buga a kasar, da suka hada da ittafan adabi da na wakoki, daga ciki har da diwanin, Hafez, da na Sa’adi, da Kheyam, da Maulawi, da Masnawi.

Wannan baje kolin littafai na duniya zai ci gaba da gudana  akasar ta Thailand daga nan har zuwa karshen makon da muke ciki.

3703226

 

 

 

 

captcha