IQNA

Jami’an Tsaron Tunusia Sun Halaka Wani Kwamandan Daesh

23:54 - April 01, 2018
Lambar Labari: 3482532
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron kasar Tunusia sun halaka wani babban kwandan kungiyar yan ta’adda ta Daesh.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar Sky News ta bayar da rahoton cewa, jami’an tsaron kasar Tunusia sun samu nasarar halaka wani babban jigo kuma kwamanda na kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh.

Bayanin ya ce jami’an tsaron sun kaddamar da farmaki a wani gida da kwamandan ‘yan ta’adda yake ciki a kusa da tsaunuka Salum, a cikingundumar Hasil Farid a arewa maso yammacin kasar.

Bayan kisan wannan gagarumin ta’addan kungiyar wahabiyawan  Daesh, an kuma samu Karin wasu bayanai da suka taimaka wajen murkushe wani shirin ‘yan ta’addan a yankin arewacin kasar.

3702572

 

captcha