IQNA

Littafin (Kauna a cikin Kur’ani) A Baje Kolin Littafai Na Alkahira

23:56 - February 02, 2018
Lambar Labari: 3482358
Bangaren kasa da kasa, an nuna littafin (Kauna a cikin Kur’ani) na Ghazi bin Muhammad bin Talal Hashemi a baje kolin littafai na birnin Alkahira.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an nuna littafin (Kauna a cikin Kur’ani) a baje kolin littafai na birnin Alkahira a bangaren littfan cibiyar Azhar.

Marubucin wannan littafi ya kasa shi bangaror biyar, da suka hada da son Allah, son manzon Allah (SAW) son mutum, bincike kan s da abin da ake so, da kuma manufar halitta, inda yake bayyana cewa mutum an halicce da wannan sirri na son wani abu ko akasin haka a cikin lamirinsa, wanda kuma son Allah da tafiya zuwa gare shi, shi ne hakikanin manufa.

A daya bangaren kuma an nuna wani littafin wanda yake magana a kan yanayin da musulmin Rohingya suka samu kansu a kasar Myamar, da kuma yadda duniya ta nuna halin ko in kula kan halin wadannan musulmi suka samu kansu a ciki.

Bugu da kari kan hakan, littain ya nuna aibu kana bin da muuslmi suka yi kan batun na Rohingya, inda wasu kasashe ‘yan kalilan ne kawai suka nuna damuwarsu da kuma bayar da taimakon da za su iya, amma wasu manyan kasashen msuulmi masu takama da kudi da man fetur, ko a jikinsu ba nuna damuwa ba balantana su bayar da taimakon da ake bukata ga wadannan bayin Allah.

3687592

 

 

captcha