IQNA

Tawagogi Fiye Da 10,000 Ne Za Su Halarci Taron Arbaeen

22:03 - November 04, 2017
Lambar Labari: 3482064
Bangaren kasa da kasa, Bangaren da ke kula da harkokin tarukan arbaeen na Imam Hussain (AS) ya sanar da cewa, cibiyoyi fiye da 10,000 ne suka yi rijistar sunayensu domin hidima a lokacin wadannan taruka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hulda da jama'a a hubbaren Imam Hussain (AS) cewa, Rayadh Ni'amah Salman ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu cibiyoyi fiye da 10,000 ne suka yi rijistar sunayensu domin hidima a lokacin wadannan taruka masu albarka.

Ya ci gaba da cewa wadannan cibiyoyin za su gudanar da ayyuka na musamman a lokacin gudanar da tarukan arbaeen a Karbala, da hakan ya hada da taimaka ma marassa karfi, da kuma samar da wuraren hutawa akan hanyoyin isowa Karbala daga biranan da ake tasowa.

Haka nan kuma ya bayyana cewa dangane da lamurran tsaro jami'an tsaro sun dauki dukkanin matakan da suka dace domin bayar da kariya ga masu gudanar da tarukan.

Abin tuni a nan dais hi ne, tarukan arbaeen na Imam Hussain (AS) na daga cikin tarukan da mabiya mazhabar shi'ar Alul bai ke gudanarwa tun fiye da shekaru dubu da suka gabata, duk da cewa a wasu lokuta ana samu canje-canje da kan jawo dakatar da tarukan a wasu lokutan.

3659561


captcha