IQNA

An Bude BabbanTaron Malaman Gwagwarmaya Na Duniya A Beirut

23:42 - November 02, 2017
Lambar Labari: 3482059
Bangaren kasa da kasa, an bude babban taron malaman gwagwarmaya na duniya a birnin Beirut fada mulkin kasar Lebanon mai taken nuna goyon baya ga Palastine.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin alalam ya habarta cewa, an bude babban taron malaman gwagwarmaya na duniya a birnin Beirut fada mulkin kasar Lebanon mai taken nuna goyon baya ga Palastine Isra’ila kuma kan hanyar rushewa.

Wannan taro shi ne karo na biyu da aka gudanar da tare da halartar malamai da masana daga kasashen duniya 60, wadanda suka suke gabatar da bayanai da kuma kasidun da suka rubuta a kan take daban-daban da ke da alaka da taron.

Babban abin da taron ya mayar da hankali a kansa dais hi ne, yadda za a kaucewa hankoron da wasu kasashen larabwa tare da hadin baki da Isa’ila da wasu kasashen turai suke yi, na neman kautar da hankulan al’ummar musulmi musamman larabawa daga batun Palastinu.

Taron ya jaddada cewa, batun Palastinu shi ne batu na farko a cikin al’ummar musulmi, duk hankoron da wasu kasashen turai gami da wasu ‘yan koransu daga cikin larabawa suke yin a kautar da hankulan duniya daga batun Palastinu wajibi ne a kalubalance shi.

Haka nan kuma taron ya yi Allah wadai a kan shirin da wasu kasashen larabawa suke da shi na neman kulla alaka a bayyane tare da Isra’ila, musaman ma wamnatin saudiyya, wadda ta yi nisa a cikin hakan.

3659010


captcha