IQNA

An Bude Reshen Cibiyar Kur’ani Ta Hubbaren Hussaini A Bagdad

23:32 - April 17, 2017
Lambar Labari: 3481413
Bangaren kasa da kasa, an bude wani babban reshe na cibiyar kur’ani da ke karkashin hubbaren Imam Hussain a birnin Bagadaza tare da halartar Hamed Shakernejad.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na Qaf cewa, a jiya an bude reshen cibiyar kur’ani da ke karkashin hubbaren Imam Hussain a birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki.

An gudanar da taron bude reshen cibiyar ne a husainiyar Bidhat Tahira da ke yankin Shu’ula a cikin birnin na Bagadaza, tare da halartar fitaccen makarancin kur’ani dan kasar Iran Hamed Shakernejadm da kuma Usama karbalai dan kasar Iraki.

Wannan taro dai ya samu halartar malamai da jami’an Iraki a cikin birnin na bagadaza da ma wasu yankuna na kasar Iraki, gami da weasu daga cikin fitattun makaranta kur’ani da kuma masu wakokin bege ga manzo da iyalan gidansa.

Ita dai wannan cibiya tana daga cikin manyan cibiyoyi da suke gudanar da ayyuka da suka shafi kur’ani a fadin kasar ta Iraki, inda sukan gabatar da taruka da nufin kara yada lamarin kur’ani a tsakanin al’ummar musulmi na kasar Iraki, da ma wasu kasashen ketare.

3590376







captcha