IQNA

An Sayar Da Kur'ani Rubutun Hannu Dala Dubu 25 A Morocco

21:35 - April 12, 2017
Lambar Labari: 3481398
Bangaren kasa da kasa, an sayar da wani dadaen kwafin kur'ani mai tsarki a kan kudi dala dubu 25 wanda aka rubuta shi da hannu daruruwan shekaru da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na khabarmasar.com cewa, an gudanar da zaman budaddiyar kasuwar sayar da dadaddin littafai a Morocco.

A wurin an nuna kwafin litatfai da suka hada da kur'anai da ke komawa zuwa ga karni na 16 miladiyya, wadanda adadinsu ya kai 207 da aka baje su a gaban mutanen da suka taru a wurin.

An sayi daya daga cikin kwafin kur'anan da aka nuna a wurin a kan kudi dala dubu 25, wannan kwafin kur'ani yana da shafuka 313, kuma kowane shafi yana da layuka 32 a cikinsa na rubutu.

Haka na kuma tsawonsa da fadinsa ya kai Cm 26x22 kamar yadda aka adana shi a cikin wani bango mai kwari.

Wannan kwafin kur'ani dai mallakin wasu iyalai ne da suka gaje shi daga kakanninsu, wanda aka rubuta shi da rubutun Morocco da Andalus.

Wannan baje koli wanda shi ne irinsa na farko da aka taba gudanarwa a kasar Morocco, yan agudana ne a birnin kazablanka, daya daga cikin manyan biranan kasar da ke karbar baki daga kasashen duniya.

3588922
captcha