IQNA

Kungiyar OIC Za Ta Gudanar Da Zama Kan Halin Da Musulmin Mayanmar Ke Ciki

22:47 - January 04, 2017
Lambar Labari: 3481102
Bangaren kasa da kasa, Ministocin harkkin waje na kungiyar kasashen musulmi ta OIC za ta gudanar da zaman gaggawa kan halin kunci da musulmin Rohingya suke ciki a kasar Myanmar.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarat cewa, Kamfanin dillancin labaran Arakan ya bayar da rahoton cewa, kungiyar OIC ta sanar da ranar 19 ga wannan wata na Janairu a matsayin ranar da ministocin harkokin wajen kasashen wannan kungiya za su gudanar da zama domin yin dubi a kan halin da musulmi suke ciki a kasar Myanmar.

Kungiyar kasashen msuulmin ta OIC dai ta yanke wannan shawara ne biyo bayan matsin lamba a kanta daga wasu daga cikin kugiyoyin kare hakkin bil adama na kasashen musulmi da wadanda ba, da ke neman ta dauki mataki na taka wa mahukuntan Myanmar birki kan cin zarafin da suke yi wa musulmi.

Mai magana da yawun kungiyar Maha Akil ta bayyana cewa, za a gudanar da zaman ministocin harkokin wajen kungiyar kasashen msuulmin ne a birnin Kualampour fadar mulkin kasar malaysia, inda ta ce suna da dukkanin bayanai kan irin cin zarafi da kisan gilla da sauran keta hurumin bil adama da aka aikata kan musulmin kasar Myanmar, wanda kuma a zaman ne za a san matakin da za a dauka na bai daya kan batun.

Ta ce yanzu abin da ke gabansu a matsayin mataki na farko shi ne isar da taimakon gaggawa na abinci da kayyakin bukatar rayuwa musulmin kasar ta Maynamar da ke cikin mawuyacin hali.

3559802


captcha