IQNA

​Jagora: Iran Ta Taka Rawa Wajen Hana Masu Girma Kai Cimma Bakaken Manufofinsu

14:45 - September 04, 2022
Lambar Labari: 3487797
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin Musulunci na Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa, a yau ma'abota girman kai sun gane cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kawo cikas wajen aiwatar da dama daga cikin bakaken manufofinsu a kanta, da ma a yankin gabas ta tsakiya.

A jawabin da ya gabatar a yayin karbar mahalarta taro karo na 7 na "Majalisar Ahlul Baiti ta duniya a Tehran,Ayatollah Ali Khamenei ya ce: “mabiya mazhabar Ahlul bait suna alfahari da tsayin daka da suka yi wajen adawa da mulkin mallaka, da kuma dakatar da cimma manufofinsu wajen yin katsalandan a cikin harkokin kasashe, da gwamnatoci, ta hanyar kama-karya."
Ya kara da cewa: A yau su da kansu sun yarda cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sha gabansu, kuma sun kasa durkusar da ita ko kuma mayar da ita ‘yar amashin shata.
Ya ce "haushinmu da ma'abota girman kan suke ji, da kuma kiyayyar da suke yi mana, hakan ya samo asali ne daga kwarin gwiwar da muka samu wajen ci gaba da yin tsayin daka, da kuma yadda hakan ya yi tasiri ga wasu kasashe har su ma suka bi irin wannan salon a kin mika kai ga ‘yan mulkin mallaka.”
Ya ci gaba da cewa, kirkiro kungiyoyin ‘yan ta’adda da hukumomin leken asirin Amurka da kawayenta suka yi, duk yana daga cikin shirinsu na aibanta musulmi da kasashen musulunci, duk kuwa da cewa hakan ya kara fito da maitarsu a fili, kuma musulmi a ko’ina cikin fadin duniya suna ta kara fadaka game da wannan makirci da ake shirya musu.

http://hausatv.com

captcha