IQNA

Gyaran Tagogin Masallacin Quds Mai Alfarma

14:39 - November 20, 2021
Lambar Labari: 3486581
Tehran (IQNA) Wasu gungun Falasdinawa da ke ayyuka karkashin kulawar kwamitin gyaran masallacin Al-Aqsa na aikin sake gyaran tagogin masallacin da suka karye.

A rahoton da shafin Madison ya bayar, ana ci gaba da aikin gyaran tagogin Masallacin Al-Aqsa da masu fasahar ayyukan gyare-gyare Falasdinawa suke yi.

Tsoffin gilassan wasu tagogin masallacin Al-Aqsa sun farfashe sakamakon hare-haren baya bayan nan da dakarun yahudawan sahyuniya suka kai kan Falasdinawa a masallacin Al-Aqsa.

An yi waɗannan tagogin ne da gilashi, ina masu ayyukan fasaha Falasdinawa suke gyara tagogin a cikin ayyukan na musamman da kwamitin ke aiwatarwa.

Ayyukan gyaran waɗannan tagogi ana yin su gaba ɗaya da hannu, kuma wani lokacin kuma yana ɗaukar watanni 6.

Wadannan tagogi suna kara wa ginin masallacin kyau, kuma an zana ayoyin kur'ani da hadisai na annabi a kansu.

4014659

 

 
captcha