IQNA

Jawabin Jagoran Juyin Musuluni Na 19 Dey:

Dole Amurka Ta Janye Dukkanin Takunkuman Da Ta Kakaba Wa Iran Kafin Komawa Ga Yarjejeniyar Nukiliya

21:43 - January 08, 2021
Lambar Labari: 3485534
Tehran (IQNA) jagoran juyin juya halin musuluni a Iran ya bayyana abin kunyar da ya faru a Amurka da cewa shi ne hakikanin Amurka, ba abin da wasu suke tsammani ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar rikicin siyasa da zaɓe bugu da ƙari kan take haƙƙoƙin bil’adama da ake yi a Amurka ya kawo ƙarshen dodoridon da take yi wa al’ummomin duniya.

Jagoran ya bayyana hakan ne cikin wani jawabin da yayi yau ɗin nan Juma’a don tunawa da zagayowar yunƙurin al’ummar garin Qum na Iran a shekarar 1978 don tinƙarar gwamnatin kama karya ta Shah a ƙasar Iran, inda ya ce a yau dai muna ganin irin yadda wannan ‘yar dodoridon ta koma. Wannan ita ce demokradiyyarsu. Wannan shi ne tsarin zaɓensu, sannan kuma wannan shi ne kare haƙƙoƙin bil’adaman da suke ikirarin suna yi. suna kashe baƙin fata guda cikin wasu sa’oi ko ranaku, sannan kuma ba a hukunta wanda yayi kisan gillan.

Jagoran ya ce abin baƙin cikin shi ne cewa har ya zuwa yanzu wasu suna bautar Amurka, yana mai cewa wasu suna tunanin idan har muka shirya da Amurka shi kenan ƙofar Aljanna ta buɗu mana. Jagoran ya ce Amurka tana ganin za ta iya tabbatar da maslaharta ce ta hanyar haifar da rikici da rashin tabbas a yankin Gabas ta tsakiya, don haka ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da haƙƙin ƙarfafa kanta don ta samu damar kare kanta daga wannan barazana ta maƙiya.

Yayin da ya ke magana dangane da tasirin Iran a yankin Gabas ta tsakiya wanda makiyanta suke ganin ganin bayan hakan kuwa da kuma tsayin dakanta wajen taimakon dukkanin waɗanda ake zalunta, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewa Iran tana nan daram wajen ci gaba da goyon bayan ƙawayenta na yankin, yana mai cewa kasantuwar Iran a ɓangarori daban-daban na yankin kuwa don tabbatar da tsaro da zaman lafiyan yankin ne.

Yayin da ya ke magana dangane da maganar da maƙiyan Iran suke yi na neman tattaunawa da ita kan ƙarfin da take da shi na kariya da kuma makamai masu linzami, Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi watsi da wannan batun yana mai cewa Iran tana da haƙƙin mallakar ƙarfin kare kanta daga barazanar maƙiya kuma ba za ta taɓa yin wasa da hakan ba.

Dangane da batun dawowar Amurka cikin yarjejeniyar nukiliya kuwa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar Iran dai ba ta wata gaggawa kan dawowar Amurka cikin yarjejeniyar, abin da kawai take ƙoƙarin gani shi ne ɗauke mata takunkumin zalunci da aka ɗora mata. Jagoran ya nuna goyon bayansa ga ƙudurin da majalisar shawarar Musulunci ta ƙasar Iran ɗin ta ɗauka na kawo ƙarshen takunkumin da aka sanya wa ƙasar Iran lamarin da ya sanya a kwanakin baya gwamnatin Iran ɗin dawo da shirin da take da shi na tace sinadarin uranium ha zuwa kashi 20%.

Tun da farkon jawabin nasa dai sai da Jagoran ya jinjina wa al’ummar Iran da ma ƙasar Iraƙi dangane da irin gagarumin bukukuwan da suka gudanar don tunawa da zagayowar shekara guda da shahadar Janar Qasim Sulaimani, tsohon kwamandan rundunar ƙudus ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci na ƙasar Iran da kuma shahid Abu Mahdi Al-Muhandis, mataimakin kwamandan dakarun Hashd al-Sha’abi na ƙasar Iraƙi. Kamar yadda kuma ya jinjinawa Shahid Muhsin Fakhrizadeh, kwararren masanin nukiliyan Iran da aka kashe a kwanakin baya.

3946372

 

 

 

 

 

 

 

captcha