IQNA

Jagoran Juyin Musulunci Na Iran:

Gudunmawar Ma’aikatan Jinya A Lokacin Corona Ta Kara Daukaka Matsayinsu A Wurin Al’umma

23:33 - December 20, 2020
Lambar Labari: 3485475
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya yi jinjina ta musamman ga ma'aikatan jinya sakamakon sadaukarwar da suke yi domin ceton rayuwar jama’a, tare da bayyana abin da suke yi da cewa jihadi ne.

Jagoran ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da ya gabatar a yau, domin tunawa da ranar ma’aikata masu jinya, wadda ake ba ta muhimmanci matuka a kasar Iran.

Ya ce ko shakka babu ma’ikatan jinya suna da matsayi na musamman a cikin kowace al’umma ta duniya, amma a wannan karo hakikanin matsayinsu na masu sadaukarwa domin ceton rayuwar al’umma ya kara bayyana a wannan lokaci da ake fama da annobar corona.

Haka nan kuma ya bayyana cewa, baya ga aiki na kula da jikin marassa lafiya da yi magani, suna da wani aiki maimuhimmanci wanda shi ne karfafa maras lafiya tare da sanya shi nishadi, domin rage masa damuwar da take da shi, wanda kuma wannan abu ne da addinin muslunci ya yi umarni da shi.

Dangane da hakkokin masu aikin jinya kuwa, jagoran ya bayyana cewa abu ne da ya rataya a kan jami’an gwamnatin kasa, domin kuwa shi mai aikin jinya shi ne yake tare da maras lafiya fiye da likita, saboda haka yana bukatar a dauke masa abubuwa da dama ta fuskar rayuwarsa domin ya mayar da hankali ga aikin kula maras lafiya.

Haka nan kuma ya bayar da misali kan yadda masu kula da maras lafiya akowane a asibiti suka fi zama wadanda cuta tafi saurin kamawa, musamman a wannan zamani da ake fama da corona, inda masu aikin jinyar marassa lafiya da dama suka kamu, wasu ma suka rasa rayuwarsu a wannan aiki.

Daga karshe jagoran ya yi fatan alhairi ga dukkanin al’umma musamman masu sadaukarwa domin sauran al’umma su ci gaba da kasancewa a raye a cikin koshin lafiya, wanda kuma ma’aikatan jinya da likitoci da sauran bangarori na kiwon lafiya suna gaba a wannan bangare.

3942124

 

captcha