IQNA

An Saki Wasu Ma’aikatan Cibiyar Muslunci Da Aka Sace A Kenya

23:00 - August 27, 2020
Lambar Labari: 3485125
Tehran (IQNA) An saki mutanen da suke aiki a wata cibiyar musulunci a birnin Nairobi na kasar Kenya bayan sace sun a tsawon kwanaki.

Shafin Standard Media ya bayar da rahoton cewa,  saki mutanen da suke aiki a wata cibiyar musulunci a birnin Nairobi na kasar Kenya bayan sace su na tsawon kwanaki goma sha biyu.

Bayanin ya ce daga cikin mutanen uku akwai daraktan cibiyar, da kuma wasu maa’ikata biyu, wadanda aka sace su tun ranar 15 ga watan Agusta, ba tare da sanin dalilin hakan ba.

Amma a ranar Litinin da ta gabata an kawo su a kusa da birnin Nairobi aka sake su, amma idanunsu a  rufe, sai dai jami’an ‘yan sanda sun sanar da cewa suna gudanar da bincike kan lamarin, domin gano wadanda suke da hannu a cikin wannan lamari.

 

3919415

 

captcha