IQNA

Cibiyar Darul Fatwa Ta Masar Ta Yi Allawadai Da Hare-Haren Turkiya A Kan Syria

23:45 - March 03, 2020
Lambar Labari: 3484581
Tehran – (IQNA) babbar cibiyar bayar da fatawoyin muslunci a kasar Masar ta yi tir da Allawadai da hare-haren wuce gona da iri da Turkiya take kaddamarwa kan kasar Syria.

Shafin Arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da cibiyar darul fatwa ta fitar a yau, ta yi Allawadai da kakkausar murya kan shishigin da Turkiya take yi kan kasar Syria.

Kwamitin da ke sanya idi kan ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke karkashin cibiyar ne ya harhada rahoto kan ayyukan soji da Turkiya take gudanarwa a cikin kasar, inda rahoton ya tabbatar da cewa Turkiya tana mara baya ne ga kungiyoyin ‘yan ta’adda da ake yin amfani da su domin rusa kasar ta yria tsawon shekaru tara.

Rahoton ya ce babbar manufar Turkiya ita ce sake dawo da daular kama karya ta Usmaniyya a kan kasashen larabawa, a kan haka ne ta dage wajen mara baya ga kungiyoyin ‘yan ta’adda irin Daesh da makamantansu domin rusa kasashen Syria da Libya.

Daga karshe bayanin ya bukaci dukkanin kasashen larabawa da kuma sauran kasashen duniya, da su dauki mataki na bai daya wajen takawa kasar ta Turkiya burki a kan mara baya ga ayyukan ta’addanci domin rusa kasashen larabawa.

 

3882921

 

 

 

 

captcha