IQNA

Rasha Ta Fitar Da Adadin 'yan Ta'adda Da Ke Syria

23:57 - August 28, 2019
Lambar Labari: 3483996
Bangaren kasa da kasa, Rasha ta bayani kan adadadin 'yan ta'adan da suka yi saura a halin yanzu a cikin kasar Syria.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Jami’in diplomasiyyar kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Ginady Kozmin wanda ya gabatar da jawabi a jiya Talata zauren Majalisar, ya bayyana cewa; Da akwai ‘yan ta’addar da adadinsu ya kai 3000 da suke a cikin kasar Syria a yanzu.”

Jami’in diplomasiyyar kasar ta Rasha ya kara da cewa; Ba ya ga ‘yan kungiyar Da’esh da kawai wasu kungiyoyin ‘yan ta’addar da suke a cikin kasar ta Syria.

A cikin makwannin bayan nan ne dai sojojin Syria wadanda na Rasha ke taimakawa su ka bude kai hare-hare akan sansanonin karshe da ‘yan ta’addar suke da ita a cikin kasar.

Tun a 2011 ne dai kasar Syrai take yakar ‘yan ta’addar da suke samun goyon baya daga Amurka, HKI, Wasu kasashen turai da na Larabawa, kamar Saudiyya da Qatar.

Ya zuwa yanzu kasar ta Syria ta sami nasara akan mafi yawancin ‘yan ta’addar, musamman kungiyoyin “Dae’sh, da Nusrat.

3838192

 

captcha