IQNA

Shugaban Kasar Kenya Ya Yi Buda Baki Tare Da Musulmi A Nairobi

23:56 - June 02, 2019
Lambar Labari: 3483701
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya yi buda baki tare da musulmi a babban masallacin birnin Nairobi a daren jiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Cameroon Journal ya bayar da rahoton cewa,a  jiya shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya halarci taron buda baki tare da musulmi a babban masallacin birnin Nairobi.

A lokacin da yake jawabia  wurin taron buda baki, Uhuru Kenyatta ya bayyana farin cikinsa maras misiltuwa, na kasantuwarsa tare da musulmi a  cikin masallaci suna cin abincin buda baki.

Ya ce ko shakka babu, hadin kai da ke tsakanin dukkanin al’ummar kasar Kenya musulmi da wadanda ba musulmi ba, da kuma yadda suke bayar da himma tukuru a dukkanin bangarori a tare, shi ne babban sirrin dukkanin ci gaban da kasar ta samu.

Uhuru Kenyatta ya ce yana fatan wannan haduwa ta zama wani masomin kara samun kyakkayawar dantaka da alaka tsakanin dukkanin bangarori na al’ummar kasar Kenya.

Sheikh Muhammad warfa babban limamain masallacin ya zagaya da shugaba Uhuru Kenyatta a dukkanin bangarori na masallaci, da suka hada da babban dakin karatu na masallacin, da kuma cibiyar ilimi ta musulmi da ke hade da ginin msallacin.

 

3816405

 

 

 

captcha