IQNA

Rasha Ta Aike Da Kayayyakin Aikin Asibiti Na Zamani Zuwa Syria

23:50 - March 27, 2019
Lambar Labari: 3483498
Gwamnatin kasar Rasha ta aike da kayayyakin aikin asibiti na zamani zuwa kasar Syria.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, a jiya wasu manyan jiragen daukar kaya mallakin rundunar sojin kasar Rasha sun isa yankin Tartus na Syria.

Shugaban bangaren bayar da agaji na sojojin kasar Rasha manja Janar Danis Ivanov ya fadi jiya cewa, babbar manufar kai wadannan kayayyaki zuwa kasar Syria ita ce taimakawa wajen farfado da ayyukan gagagwa a sibitocin kasar da aka rusa sakamakon yakin da aka haddasa a kasar.

Ya ce mafi yawan kayan da suka tura Syria sun shafi kayan ayyukan kula da kananan yara ne da suak samu munanan raunuka sakamakon yakin. Da kuma wasu kayan ayyukan tiyata na musamman da ake bukatarsua  asibitocin kasar ta Syria.

Baya ga haka kuma akwai likitoci daga kasar Rasha wadanda za su taimaka wajen ci gaba da gudanar da ayyuka na musamman da ake bukatar kwaarrun likitoci a  kansu a kasar ta Syria.

Bababn jami’in na rundunar sojin Rasha bangaren bayar da agajin gagawa ya bayyana cewa, baya ga samar da wadaan kayayyaki, za su kuma taimaka wajen gyara wasu daga cikin asibitocin da ‘yan ta’adda suka rusa a kasar ta Syria nan bad a jimawa ba.

 

3799802

 

 

 

captcha