Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, saurin igiyar ruwan wacce ake kira tsunami ta kai kilomita dari takwas a ko wace sa'a sannan ta na da tsawon mita shida.
Ambaliyar ruwan da tsunamin ta jawo ya rusa gidaje, tituna da gadoji a yankin, banda haka sun jawo katsewar wutan lantarki da kuma wayar tarko a yankin.
Jami'an bada agajin gaggawa sun bayyana cewa mutane dari uku da tamanin ne aka tabbatar da mutuwarsu sannan wasu dari biyar da arbain suka ji rauni a yayinda wasu 29 suka bace.
Shugaban kasar ta Indonasia ya ziyarci wurin don ganewa idanunsa irin halin da mutanen yankin suka shiga ciki. An rufe tashar jiragen sama na yankin a jiya jumma'a sanadiyyar lalacewar da kayakin aiki a wajen suka yi sanadiyar girgizan kasar da Tsunami.
Amma ana saran za'a bude shi a yau Asabar don samun damar kai kayakin agji na gaggawa wadanda suka hada da abinci da ruwan sha.