IQNA

Inshorar Lafiya Ta Musulmi Ta Samu Karbuwa A Kenya

23:53 - September 05, 2018
Lambar Labari: 3482954
Bangaren kasa da kasa, kamfanin inshorar lafiya mallakin musulmin kasar Kenya ya samu karbuwa a tsakanin al’ummar kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar The Nation cewa, inshorar lafiya ta musulmin kasar Kenya wato Takaful ta samu karbuwa a tsakanin al’ummar kasar musulmi da wanda ba musulmi ba.

Cibiyar da ke kula da ayyukan kamfanonin inshorar lafiya a kasa Kenya AKI ta sanar da cewa, inshorar takaful ita ce inshorar da tafi saurin samun karbuwa a tsakanin al’ummar Kenya a halin yanzu.

Wannan tsarin inshore ana gudanar da shi ne bisa kiyaye kaidoji na addinin muslunci, ta yadda duk wanda yake amfana da wannan inshore sharadi ya kiyaye wadannan kaidoji.

Baya ga haka kuma akwai saukakawa ga jama’a a cikin tsarin wannan inshora, wanda hakan ya sanya jama’a da dama a kasar Kenya yin amfani da ita.

3744200

 

 

 

 

 

 

 

captcha