Tashar talabijin ta Alwatan ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban wani taro da yahudawa suka shirya a Faransa, Macron ya bayyana cewa amincewa da Quds a matsayin babban birnin Isra’ila baa b ne da zai taimaka wajen warware matsalar da ke tsakanin Isra’ila da Palastinawa ba.
Macron ya ce irin wannan mataki babu abin da zai kara illa dagula lamurra, maimakon hakan a cewarsa, kamata ya yi a karfafa batun tattaunawa tsakanin bangarorin biyu domin su warware matsalarsu ta hanyar fahimtar juna.
Tun bayan da Trump ya ayyana birnin Quds a matsayin babban birnin Isra’ila, yake ci gaba da shan suka daga ciki da wajen Amurka, har daga manyan kawayen Amurka na yammacin turai.