IQNA

Wanda Ya Jagoranci Sallar Juma’a A Tehran:

Yunkurin Trump Na Hada Runduna Domin Yaki Da Iran / Kare Tsarin Musulunci Shi Ne Muhimmi

23:40 - December 22, 2017
Lambar Labari: 3482224
Bangaren kasa da kasa, Ayatollah Imami ashani wanda ya jagoranc sallar Juma’a a Tehran ya bayyana cewa, Trump na hankoron ganin ya hada runduna domin tunkarar Iran, bayan shirga karya kan cwa Iran na mika makamai ga ‘yan gwagwarma a yemen domin kaiwa al saud hari.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Limamin da ya gabatar da sallar jumma'a a yau a nan birnin Tehran ya bayyana cewa babu wata shaida wacce ta nuna cewa Iran ce ta mikawa mayakan Huthi makamai masu linzami kamar yadda gwamnatin kasar Amurka take riyawa.

Ayatollah Imami Kashani ya bayyana haka ne a cikin khudubibunsa na Jumma'a a yau a nan birnin Tehran. Aya. Imami Kashani ya kara da cewa, gwamnatin kasar Amurka ta sayarwa kasar Saudia makamai na billiyoyin dalar Amurka don ta hana zaman lafiaya a yankin gabas ta tsakiya kamar yadda take yi a halin yanzu a kasar Yemen, amma kuma tana sun mutanen kasar su zauna ba tare da yin wani kokarin na kubutar da kansu daga hannun wadanda suke zaluntarsu ba. 

A wani bangare na khudubarsa Aya. Imami Kashani ya ce shugaban Amurka Donald Trump ya kaskanta mutanen kasar Amurka tare da mummunan halayensa na wulakansa abubuwan da dukkan duniya suke mutunta wa. Limamin ya kara da cewa gwamnatin Amurka ba zata taba cimma burinta na maida birnin Qudus a matsayin cibiyar gwamnatin HKI ba. 

Daga karshe limamin ya kammala da cewa gwamnatin kasar Amurka tana takurawa Iran ne ba wai don su Iraniyawa ba ne, sai dai don addininsu wanda suka zaba, yake kuma iko a kasarsu.

3675076

 

 

captcha