Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na
Alwatan cewa, bayan jin cewa an tabbatar da hukuncin kisa a kansa
Ayatollah Nimr Baqir Nimr ya ce; ya mika lamarinsa ga ubangiji.
Bayan jin cewa an tabbatar da hukuncin kisa a kansa sai ya aike da wasika zuwa ga mahaifiyarsa da ke cewa:
Zuwa ga mahaifiyata Ummu Ja'afar;
Mahaifiyata
ina godiya ga Allah kan duk abin da ya kaddara mani, Allah shi ne yafi
sani a kan komai da ya shafi da kuma karshen lamarinmu, duk abin da
Allah ya zama a kanmu shi ne mafificin zabi da kuma mafi alkhairi gare
mu, muna yin zabi, amma Allah yana zabar mana abin da ya fi a gare mu.
A
lokacin da ya zama Allah shi ne mai jibintar lamarina kuma yake sane da
halina, wannan shi kadai ya ishe ni, Allah shi ne mahaliccinmu baki
daya, kuma shi ne ya tsara tare da kaddara komai da ya shafi rayuwarsu.
Babu
wani wanda ya isa ya aikata wani abu a cikin duniyar nan face da sanin
Allah, babu wani abu da ke wajen sanin Allah da ikonsa, mahaifiyata ina
rokon Allah yak are ki ya kuma kare dukkanin bayinsa.
3472915