IQNA

An kawo karshen matakin share fage na gasar kur'ani ta kasa da kasa a kasar Saudiyya

16:40 - September 12, 2022
1
Lambar Labari: 3487843
Tehran (IQNA) An kawo karshen matakin share fage na gasar kur'ani ta kasa da kasa a kasar SaudiyyaTehran (IQNA) An kawo karshen matakin share fage na gasar kur'ani mai tsarki karo na 42 na Sarki Abdulaziz a kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Youm cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini, da’awah da shiryarwa ta kasar Saudiyya ta sanar da kawo karshen matakin share fage na gasar haddar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa.

Alkalan kotun sun saurari karatuttukan masu inganci guda 153 da suka wakilci kasashe 111 na duniya tare da tantance ayyukansu na haddar karatu da tafsiri.

Haka kuma an gudanar da wadannan gasa ne da nufin daukaka matsayin gasar, da kara sha'awar mahalarta da wadanda suka cancanta a masallacin Harami tare da halartar kwamitin shari'a na kasa da kasa.

A yau Litinin 12 ga watan Satumba ne za a fara gasar karshe a masallacin Harami, kuma wadanda suka yi nasara a matakin share fage za su fafata da juna safe da yamma.

Za a ci gaba da wannan gasar har zuwa ranar Alhamis mai zuwa.

4085100

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasashe duniya cancanta
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Abubakar abdul.aziz
0
0
Toh Allah yayi taimako ya kuma karawa dalibanmu ilimi wanda zai anfani musulinci
captcha