IQNA

An Girmama Wata Dalibar Jami’a da ta rubuta Kura'ani a kasar Masar

17:55 - May 19, 2022
Lambar Labari: 3487313
Tehran (IQNA) Wata daliba a jami'ar Azhar mai haddar kur'ani ta samu damar rubuta kur'ani mai tsarki a karon farko cikin watanni hudu da rabi.

A cewar Khalid, Hajar Abdul Raouf Abdul Halim, wacce ta kammala karatu a tsangayar ilimi ta jami’ar Al-Azhar wadda ta kammala karatun digiri a jami’ar, ita ce ‘yar kasar Masar ta farko da ta fara rubuta kur’ani da hannu, mafarkin da ta ce ta dade tana yi.

Hajar, wadda ke zaune a  birnin Daru a lardin Aswan, ta ce bisa kwarin gwiwar da mahaifinta ya bata, wannan  ya sa wannan buri  nataya cika cikin watanni hudu da rabi kuma ta samu damar rubuta kur’ani a alkalami da kuma salon rubutu “Ottoman.

A wata hira da aka yi da ita a gidan talabijin, ta bayyana cewa ta yi wannan aiki ne da daddare domin ta yi amfani da yanayin kwanciyar hankali da natsuwa.

Nagartar wannan aikin yana komawa ne zuwa ga mahaifina, wanda ya sa gaba wajen karaffa gwiwa ta.

Manufar rubuta Alkur’ani ita ce ta kasance mai inganci kuma abin koyi ga ‘ya’ya mata na al’umma, kuma ta yi haka ne kawai don neman yardar Allah Ta’ala da samun lada a Lahira.

 

https://iqna.ir/fa/news/4058159

 

captcha