Baje kolin kur'ani na kasa da kasa karo na 29 a Tehran
Tehran (IQNA) – An bude bikin baje kolin kur’ani na kasa da kasa karo na 29 a nan Tehran a ranar 16 ga watan Afrilu da muke ciki
Ana ci gaba da gudanar da baje kolin kur’ani na kasa da kasa karo na 29 a birnin Tehran na kasar Iran wanda aka bude tun daga ranar 16 ga watan Afrilu wanda zai ci gaba da gudana har zuwa ranar 29 ga watan na Ramadan mai alfarma.