IQNA

Ana Gudanar Da Gyaran Wasu Takardun Tsohon Kur'anai Na Tarihi A Hubbaren Imam Alawi

22:50 - December 01, 2021
Lambar Labari: 3486631
Tehran (IQNA) cibiyar da ke kula da kayan tarihi ta hubbaren Imam Ali (AS) tana aikin gyaran wasu daddun kwafin kur'anai.

Sashen adana rubuce-rubuce da takardu masu alaka da hubbaren Alawi  ya sanar da cewa, ana dawo da wani tsohon kur'ani mai tsarki da aka rubuta tun karni na 12 bayan hijira a cibiyar.

Hussein al-Sheibani, shugaban sashen, ya ce game da kokarin da aka yi na maido da wannan tsohuwar taswirar kur'ani: ya zama wajibi a gudanar da aikin sake gyara takardunsa.

Ya kara da cewa: "Wannan sigar ta riga ta wuce matakai da yawa ya zuwa yanzu, kuma ana cikin mataki kusan na karshe wajen aikin, wanda zaran an kammala za a fitar das u zuwa wuraren ajiye kayan tarihi na hubbaren.

4017684

 

 

captcha