IQNA

Hukumomin Shari’a A Argentina Za Su Yi Bincike Kan Kisan Musulmin Rohingya A Myanmar

17:52 - November 29, 2021
Lambar Labari: 3486621
Tehran (IQNA) Hukumomin shari'a na kasar Argentina sun amince da bude wani bincike kan karar da aka shigar a kan sojojin Myanmar bisa zarginsu da yin kisan kiyashi a kan tsirarun 'yan kabilar Rohingya.

Jaridar Financial Times ta bayar da rahoton cewa, wannan matakin dai ya samu karbuwa ga wadanda abin ya shafa, da suke bayyana cewa wani mataki ne na tarihi na gurfanar da janar-janar na Myanmar a gaban kuliya.

Wata kungiyar Rohingya da ke da mazauni a Burtaniya ce tare da wasu mata shida da suka tsira daga harin da sojoji suka kai a jihar Rakhine a kasar Myanmar a shekarar 2017,  suka shigar da karar.

A harin da sojojin Myanmar suka kai kan tsirarun musulmi ‘yan kabilar Rohingya, jami’an sojin sun kashe dubban mutane, da kuma yin fyade gami da raba kimanin mutane 750,000 da muhallansu.

Tomás Ojea Quintana, lauyan masu shigar da kara, ya shaidawa jaridar Financial Times cewa "Muna neman sakamako mai ma'ana wajen yin wannan bincike, da kuma hukunta wadanda suka shiga cikin wannan kisan kare dangi kai tsaye da kuma a fakaice, muna so mu zakulo wadanda suka aikata wannan laifi da zimmar ganin an gurfanar da su a  gaban kuliya a Argentina.”

Quintana ya ce wadanda abin ya shafa na bukatar adalci ga shugabannin sojojin Myanmar, musamman Min Aung Hlaing, wanda ya sa ido a kan murkushe Rakhine a shekarar 2017, wanda kuma shi ne ya hambarar da gwamnatin Aung San Suu Kyi a wani juyin mulki.

Wannan shari’ar tana karkashin kotun duniya ne, ta yadda masu aikata manyan laifuka (kamar kisan kare dangi da na yaki) za a iya gurfanar da su a ko’ina a cikin duniya.

captcha