IQNA

Jaridar Isra'ila Ta Ce Suna Da Hannu Wajen Sanya Burtaniya Daukar Mataki Kan Hamas

14:47 - November 22, 2021
Lambar Labari: 3486591
Tehran (IQNA) Wata Jaridar Sahayoniyya a cikin wani rahoto da ta fitar ta tabbatar da rawar da hukumar leken asiri ta gwamnatin Isra'ila ta taka a matakin da Birtaniyya ta dauka kan Hamas a baya-bayan nan.

Jaridar Times ta Isra'ila a cikin wani rahoto da ta fitar ta bayyana irin rawar da hukumar leken asirin haramtacciyar kasar Isra'ila ta "Shabak" ta taka a matakin da gwamnatin Birtaniya ta dauka na ayyana kungiyar Hamas a matsayin kungiyar ta'addanci.

Shafin yanar gizo na jaridar ya ce kungiyar leken asiri da tsaron cikin gida ta Isra'ila da aka fi sani da Shabak (Shin Bet) ta taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan gwamnatin Birtaniyya domin ta ayyana kungiyar Hamas a matsayin kungiyar ta'addanci.

Kafar yada labaran ta Isra'ila ta kuma ruwaito cewa, jami'an leken asirin Isra'ila sun ba da bayanai ga manyan jami'an Birtaniyya game da 'yan kungiyar Hamas da kuma hanyoyin da suka ce kungiyar tana amfani da su wajen tara kudade a cikin Burtaniya da ma wajen kasar.

A cewar wannan rahoto; 'Yan kungiyar Shabak da dama sun yi tafiya zuwa Burtaniya a cikin 'yan makonnin nan, kuma bayanan da suka bayar ga takwarorinsu na Burtaniya sun taimaka wajen yanke shawarar daukar wannan mataki.

Matakin dai na Burtaniya yana ci gaba da sha kakkausar suka daga al'ummar falastinu da ma wasu kasashe masu mara baya ga Falastinu, da kuma kungiyoyi masu zaman kansu a kasashen larabawa da na musulmi.

 

4015291

 

captcha