IQNA

Taro Mai Taken Samun Masaniya Kan Annabawa 25 A Dubai

20:02 - November 16, 2021
Lambar Labari: 3486566
Tehran (IQNA) wani taro mai taken samun masaniya kan annawa 25 da ke gudana a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa.

Shafin yada labarai na arab News ya bayar da rahoton cewa, Runfar kungiyar hadin kan kasashen musulmi a baje kolin Expo 2020 Dubai ta gabatar da shafi da ke nuni da  rayuwar annabawa 25 da aka ambata a cikin Alkur'ani a cikin harsuna daban-daban guda biyar.

A wani bangare na wannan baje kolin, shirin mai taken “Annababawa kamar kuna ganinsu” an gabatar da shi ne inda aka yi amfani da fasahar zamani wajen gabatar da tarihin annabawa da manzanni na sama.

Wannan shiri yana nuni da sakonnin zaman lafiya, soyayya, kauna, hakuri, zama tare da dan Adam wadanda wadannan annabawa suka zo domin isar musu da sako.

Haka nan kuma shirin ya yi nuni da irin kyawawan dabi'un Manzon Allah (S.A.W) da kuma kamala da ke cikin sakon Musulunci ga dukkanin al'ummomi na duniya baki daya.

آشنایی با زندگی 25 پیامبر الهی در اکسپو 2020 دبی + فیلم

آشنایی با زندگی 25 پیامبر الهی در اکسپو 2020 دبی + فیلم

آشنایی با زندگی 25 پیامبر الهی در اکسپو 2020 دبی + فیلم

 

 

4013338

 

Abubuwan Da Ya Shafa: hadaddiyar daular larabawa dubai birnin
captcha