IQNA

Ana Shirin Bude Gasar Kur'ani Ta Duniya Da Ta Kebanci Mata Zalla A Dubai

16:49 - November 16, 2021
Lambar Labari: 3486564
Tehran (IQNA) ana shirin fara gasar kur’ani mai tsarki ta duniya ta mata zalla a birnin Dubai an Hadaddiyar Daular Larabawa.

​A ranar Asabar 20 ga watan Nuwamba ne za a fara gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa karo na biyar mai taken gasar kur’ani mai tsarki ta Fatemeh Bint Mubarak’ ta mata zalla a birnin Dubai na UAE kuma za a ci gaba har zuwa ranar 27 ga watan Disamba.

Ibrahim Abu Mulha mataimakin gwamnan Dubai kan harkokin al'adu ya bayyana cewa, “Wannan gasa daya ce daga cikin shirye-shiryen bayar da lambar yabo ta kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa ta Dubai, kuma tana da muhimmanci wajen kara yada lamarin littafin Allah Madaukakin Sarki, da kuma karfafa ayyukan agaji da jin kai a kasashen Larabawa da dama, da  kuma kasashen musulmi.

Ya kara da cewa: Mata masu haddar kur'ani mai tsarki daga kasashe kusan 50 suna shirin halartar wannan gagarumin taron na kur'ani mai tsarki, kuma adadin zai karu nan da kwanaki masu zuwa. 

Mahalarta taron za su isa UAE ne daga gobe 17 da 18 da 19 ga Nuwamba, sannan daga 26 zuwa 28 ga Nuwamba kuma alkalan gasar za su sanar da hukunci na karshe na karshe, alkalan dai sun kunshi alkalan kasa da kasa daga Saudiyya, UAE, Jamhuriyar Masar, Indonesiya da Pakistan.

 

4013702

 

 

captcha