Kamfanin dillancin labaran anatoli ya bayar da rahoton cewa, ana gudanar da tarukan maulidin manzon Allah a masallatan birnin Istanbul na kasar Turkiya a cikin wadannan kwanaki.
A tarukan maulidin dai ana gudanar karatun ayoyin Alkur’ani mai girma, laccoci daga malaman addini da gabatar da bayanai kan darussan da suke a cikin rayuwa mai daraja da albarka ta manzon Allah (SAW) gami da wakoki na yabia gare shi.
'Yan kasar Turkiyya suna farin ciki matuka a duk lokacin gudanar da tarukan Maulidin Manzon Allah (SAW) a masallatan Istanbul da sauran masallatai na fadin kasar, musamman masallatan tarihi, kamar masallacin Sultan Ahmed, Hagia Sophia, Sulaymaniyah da Fateh, inda ake gudanar da irin wadannan taruka.